Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada-hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Man City ta sayi dan wasan kasar Brazil mai suna Gabriel Jesus dan shekaru 19, da haihuwa akan kudi fan miliyan £27.

Dan wasan kasar Poland mai suna Bertosz ya rattaba hanu a kungiyar Leicester City na tsawon shekaru 5.

Liverpool na zawarcin Jonas Hector, daga Kungiyar kwallon kafa ta FC Koln ta kasar Jamus.

Swansea city taki amincewa da tayin da Everton tayi mata na fan miliyan £10 domin sayen dan wasanta Ashley Williams.

Shikuwa mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zidane yace yana da bukatar James Rodriguez ya cigaba da zama a Kungiyar sa ta Madrid.

Shalke 04 ta sayi dan wasan Sevilla mai suna Coke akan kudi fan miliyan £4.2.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:14 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG