Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Flying Eagles Sunyi Rawar Gani


A ci gaba da wasan kwallon kafa a gasar Olympics da ake yi a kasar Brazil, da Afirka ta Kudu sun yi chanjaras, Najeriya ta sami nasarar doke Japan da ci 5 da 4, Honduras ta doke Algeria da ci 3 da 2, yayin da Sweden suka tashi 2 da 2 da kasar Columbia.

Sauran wasannin sun hada da Portugal inda ta doke Argentina da ci 2 da nema Mexico sun tashi 2 da 2 da Jamus, yayin da Iraqi suka tashi babu ci da Denmark.

Ranar Lahadi indan Allah ya kaimu Najeriya zata fafata da Sweden inda Honduras zata hadu da Portugal, Jamus kuwa zata fafata da Koriya ne Argentina zasu buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta Algeria ne yayin da Denmark zasu fafata da kungiyar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:40 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG