Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aure Baya Hana Neman Ilimi Masamman Ga Mata


Ramatu Ibrahim Jibril
Ramatu Ibrahim Jibril

A yau dandali ya samu bakuncin Ramatu Ibrahim Jibril, wacce tayi karatu daga NCE, har zuwa digiri na biyu wato Master tana aiki da kuma auren ta.

Ta ce bata fuskanci wani matsala ba har kawo yanzu kuma aure ba ya hana mace neman ilimi idan har akwai niyyar yin karatun.

Ramatu, ta ja hankalin ‘yan uwanta mata da kada su ga kamar mace bazata iya hada neman ilimi da kula da gida ba, tace shi wannan neman ilimin zai karawa mace basirar iya tafiyar da gida da kuma tarbiyar ‘ya’yan hatta da maigidan.

Ta kara da cewa ilimi na gyara zamantakewa da makwabta domin a lokuta da dama a darushan da ake koyo akwai na sanin halaira dan Adam.

XS
SM
MD
LG