Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samari Na Guda 4 Duk Sun Mutu Bayan Mun Rabu!


Wata yarinya mai suna Tony Fenty, mai kimanin shekaru ashirin da biyar, ta bayyanar da kanta a matsayin mace da ba tada sa’a a rayuwa. Hakan ya biyo bayan yadda taga samarin ta na ta mutuwa. Ta rubuta a shafinta na zumuntar tweeter, cewar samarin ta guda hudu duk sun mutu sun barta.

A hoton da ta saka a shafin nata, inda take cewar saurayin ta na farko ya mutu a shekarar 2012, ya mutu bayan rabuwar su a matsayin saurayi da budurwa. Sai saurayin ta na biyu, wanda ya mutu a shekarar 2014, wanda shima ya mutu a dai-dai lokacin da suke shirin rabuwa.

Shi kuwa saurayin ta na uku, ya mutu bayan shekaru uku da suka rabu, shi kuwa na hudu na karshen, ya mutu ne kwanaki tara da suka wuce a dai-dai lokacin da suke soyayyar su mai dadi. Ta kara da cewar lallai wannan rayuwar ba komai bace, idan mutun bai sa tsoron mahalaccin shi a gaba ba to lallai zaiga ba dai-dai ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG