Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kare Polo Ya Kashe Jariri Dan Kwana 3 Da Haihuwa


Jami’an ‘yan sanda a garin San Diego, na jihar Califonia, a kasar Amurka, sun tabbatar da wani kisa da wani Kare mai suna Polo, yayi na wani jariri mai kwanaki uku da haihuwa. Bayan kwanaki uku da haihuwar jaririn, da mahaifiyar yaron da mahaifin shi, su na dakin hutawa suna kallon tibi, sai mahaifiyar yaron tayi attishishawa, wanda hakan ya tsoratar da Karen Polo.

A dai-dai wannan lokacin sai Karen Polo yayi kan yaron a kan gadon shi, inda yayi ma yaron jina-jina. Irin yage-yagen da Karen Polo, yayi ma yaron yasa yaron ya samu mummunan rauni, koda iyayen suka kwace yaron a hannun Karen suka garzaya asibiti, yaron ya mutu. Yanzu haka dai ana cigaba da binciken sanadiyar aukuwar abun.

A cewar jagoran binciken na hukumar ‘yan sanda Mr. DeSousa, ya bayyanar da cewar, a duk lokacin da aka samu wani kare ya ciji mutun, za’a kai shi gidajen dabbobi da za’a ajiye shi na tsawon kwanki goma. Wanda daga bisani idan masu Karen nada sauran bukata da shi, sai su nemi a basu, ko kuma idan suna so a kashe Karen sai su bada umurnin a kashe shi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG