Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Da Rashin Cikakkiyar Lafiyar Cristiano Ronaldo da Karim Benzema Zasu Taka Leda Gobe


Shahararrun yan wasan kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo da Karim Benzema, suna daga cikin ‘yan wasan da zasu buga wasan kusa da karshe na Champion League, karon farko na wannan kakar a gidan Manchester City gobe Talata in Allah kaimu, duk kuwa da yake ana shakkar cikakkiyar lafiyar.

Ronaldo wanda ya samu lambar yabon dan wasan Duniya har karo Uku, bai sami damar yin wasan da akayi ba na ranar Asabar din data gabata, inda Real Madrid ta lashe wasan da ci 3-2, amma ana tsammanin zai buga wasan gobe da zasu buga da Manchester City, tsakanin shekara ta 2003 da 2009 Ronaldo dai ya kansance da Manchester United har tsawon shekaru 6.

Ana shakku kan Benzema bayan da yaji ciwo har ya kaishi ga dangyashi kafin a tafi hutun rabin lokaci a Rayo.

Sai dai Gareth Bale ya nuna jarumtarsa alokacin da ya zarga kwallaye har biyu a raga, don farfado daga kungiyarsa alokacin da suke biyu da babu.

Shi kuma Welshman, wanda a karon farko ya dawo Ingila tun da ya bar kungiyar Tottenham shekaru uku da suka gabata, wanda kuma yayi Imanin cewa wasa na biyu da za ayi a Real Madrid shine zai taimakawa kungiyar ta fito a wasan karshe na cin Kofin Turai.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG