Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farin Jinin Mutun Nada Alaka Da Yadda Mutun Ya Gabatar Da Kanshi!


VOA Azerbaijani selfie
VOA Azerbaijani selfie

Hanyoyin samun nasarori a wajen aiki da samun karbuwa a cikin aluma suna da yawa, musamman idan mutun ya rike wasu kadan daga ciki, zai iya zama zakaran gwajin dafi a tsakanin shi da abokan shi. Babu abun da ke kara sa mutun karbuwa cikin al’uma irin mutun ya zama mai saukin kai da kokarin kyautata ma wasu, batare da ya damu da kanshi ba. Kokarin samar da maslaha da hanyoyin magance matsaloli da kan iya haifar da rashin jituwa, a tsakanin al’uma wata hanya ce da mutun zai iya samun daukaka.

Duk mutumin da ke tarayya da abokan kirki, za’a ganshi shima a matsayin mutumin kirki, domin kuwa kusantar abokan kirki, kan ba mutun damar aiwatar da abun alkhairi koda kuwa zuciyar shi ta raya mishi wani abu na daban. Amma zama cikin mutanen kirki zai sa halayyan mutun su canza matuka.

Aiki da hutawa wani muhimin abu ne ga rayuwar dan’adam, haka kuma hutu na taimakawa matuka wajen iya saka abubuwa inda suka kamata, da bada shawarwari yadda suka kamata. Don haka abune mai matukar muhimanci mutun ya dinga daukar hutu a wajen aiki, da tarayya da mutane. Yana da matukar muhinmanci mutun ya dinga nisantar inda keda hayaniya, domin hayaniya na batar da basira, da kuma saka mutun cikin dimuwa, har mutun ya kaiga manta wasu tunanin shi masu ma’ana.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG