Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Baya Ga Umurnin Addini, Ra'ayoyin Mata Akan Dalilan Da Ke Sa Samari Auren Mace Fiye Da Guda


Bayan dandalinvoa ya kammala jin ra'ayoyin samari akan dalilan da ke sa wasu matasa auren mace fiye da guda baya ga umurnin addini, a wan nan karon dandali voa ya karkata wajan 'yan mata ne domin jin nasu ra'ayin.

Kamar yadda wasu daga cikin 'yan matan suka bayyana, rashin cika al'kawari da kwadayin kayan duniya kan yaudari wasu maza domin kuwa duk yadda suke zaman lafiya da matar su, da zarar sun hadu da macen da ke da abin hannu ko iyayen ta, kwatsam sai su canza shawara.

Wasu kuma daga cikin 'yan matan sun nuna cewa yawancin samari suna da son kwai kwayon abokan su, wato abin da wane yayi su ma sai sun yi.

Daga karshe mafi rinjaye sun bayyana mana cewar wasu maza ko wanne irin zaman lafiya suke yi da matar su, sai sun kara aure saboda a cewar su, mace guda bata iya biya masu bukata.

Ga cikakkiyar hirar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG