A makon da ya gabata ne aka yi bikin daurin auren Sonam Kapoor a birnin Mumbai wanda ya samu halarcin manyan jaruman fina-finan Bollywood kamar su Salman Khan, da Shah Rukh Khan da Aishwarya Rai-Bachchan, da Akhshay Kumar da sauransu. Sonam ta auri wani dan kasuwa ne mai suna Anand Ahuja.
Wani Jean-Bernard Huon a wani kauye da ke kudancin garin Brittany, ya juya baya ga sauyi na zamani, inda shi har yanzu ya na amfani da shanu wajen yin kuda da sauran ayyuka da hannu da nufin raya al’adun da.
A wannan makon ne aka yi gasar tsallake lalatattun motoci a yammacin Sussex da ke Birtaniya inda matuka da dama suka fafata wajen fidda gwani. Wani Nick Warder ne ya zama zakaran wasan inda ya kure wata tsohuwar motar Audi ya tsallake jerin motocin mafi tsawo.
A duk shekara Kampanin GDE Bertoni ke amsar aikin sabunta kofin gasar kwallon kafa ta duniya. Sai dai kasar Italy iyakacinta kallo a gasar cin kofin ta wannan shekarar, domin a karon farko tun shekarar 1962, kasar ta gaza samun gurbin shiga wasannin.
An gudanar gasar kokawar sumo ta shagalin marabtar damina na bana a cikin jin dadi a birnin Tokyo. A tsarin kokawar, ba a yarda mata su shiga wurin da ake damben ba, saboda sun camfa cewa hakan zai gurbata wajen da suke dauka mai tsarki.
Ma'aurata sun yi tsere kan hanyoyi masu santsi da sarkakiya a kudu maso gabashin Birtaniya. Wannan wasan na kwaikwayon al'adar mutanen yankin Scandinavia na da wadanda suka kware wajen gudu sabe da matan da suka sato daga kauyukan da ke makwabtaka da su.
Jibga-jibgan Kifayen Whale Sama da 150 sun mutu yayin da ruwa ya korosu kan doron kasa, duk da irin kokarin da hukumomi suka yi na ceto rayuwarsu ta hanyar mayar da su teku guda 6 kawai suka rayu. An rufe wurin shakatawar bakin tekun yayin da hukumomi ke aikin kwashe gawarwakin kifayen da suka mutu.
Yayin da ake gudanar da zaben shugaban kasa a Masar, Heba Ragab ta goya maigidanta zuwa rumfar zabe.
Wannan macijin ana kiransa Chrysopelea a turance kuma yawanci an fi samunsa a yankin kudancin Asiya sannan ba ya da guba mai tsanani.
Yi Lodin Kari..