An gudanar gasar kokawar sumo ta shagalin marabtar damina na bana a cikin jin dadi a birnin Tokyo. A tsarin kokawar, ba a yarda mata su shiga wurin da ake damben ba, saboda sun camfa cewa hakan zai gurbata wajen da suke dauka mai tsarki.
Ma'aurata sun yi tsere kan hanyoyi masu santsi da sarkakiya a kudu maso gabashin Birtaniya. Wannan wasan na kwaikwayon al'adar mutanen yankin Scandinavia na da wadanda suka kware wajen gudu sabe da matan da suka sato daga kauyukan da ke makwabtaka da su.
Jibga-jibgan Kifayen Whale Sama da 150 sun mutu yayin da ruwa ya korosu kan doron kasa, duk da irin kokarin da hukumomi suka yi na ceto rayuwarsu ta hanyar mayar da su teku guda 6 kawai suka rayu. An rufe wurin shakatawar bakin tekun yayin da hukumomi ke aikin kwashe gawarwakin kifayen da suka mutu.
Yayin da ake gudanar da zaben shugaban kasa a Masar, Heba Ragab ta goya maigidanta zuwa rumfar zabe.
Wannan macijin ana kiransa Chrysopelea a turance kuma yawanci an fi samunsa a yankin kudancin Asiya sannan ba ya da guba mai tsanani.
A wasan farko na matakin share fage na gasar Kofin Zakaru na Hukumar wasan kwallon kafa ta Afirka na 2018.
Wani makaho dan asalin Pakistan yana wasannin hawa duwatsu da wasu tsaunuka domin nuna cewa nakasa ba kasawa ba ce.
Yi Lodin Kari..