Jibga-jibgan Kifayen Whale Sama da 150 sun mutu yayin da ruwa ya korosu kan doron kasa, duk da irin kokarin da hukumomi suka yi na ceto rayuwarsu ta hanyar mayar da su teku guda 6 kawai suka rayu. An rufe wurin shakatawar bakin tekun yayin da hukumomi ke aikin kwashe gawarwakin kifayen da suka mutu.
Yayin da ake gudanar da zaben shugaban kasa a Masar, Heba Ragab ta goya maigidanta zuwa rumfar zabe.
Wannan macijin ana kiransa Chrysopelea a turance kuma yawanci an fi samunsa a yankin kudancin Asiya sannan ba ya da guba mai tsanani.
A wasan farko na matakin share fage na gasar Kofin Zakaru na Hukumar wasan kwallon kafa ta Afirka na 2018.
Wani makaho dan asalin Pakistan yana wasannin hawa duwatsu da wasu tsaunuka domin nuna cewa nakasa ba kasawa ba ce.
Wasannin Olympics na karkara da ake yi duk shekara a jihar Punjab Da ke Arewacin India, ya janyo dubban jama’a daga sassa dabam dabam na kasar. Wadanda suka shirya wasannin sun yi ne da nufin raya al’adun ‘yan Punjab domin nunawa ‘yan baya hanya.
Matsalar beraye da ta addabi birnin Tehran ta tilastawa Iran kafa dakarun kashe beraye domin fatattakarsu. Beraye sama da miliyan 2 ne hukumomi suka ce ke cin karensu babu babbaka a birnin, adadin da ake ganin ya wuce haka. Yawaitar zubar da shara a ko'ina itace musabbabin wannan matsalar.
An kaddamar da wani babban Kumbon SpaceX na ‘yan sama jannati a jiya Talata a gwajinsa na farko dauke da wata jar motar tsere tare a yunkurin tafiyar sai baba ta gani zuwa kololuwar duniyar Mars.
Yi Lodin Kari..