A wasan farko na matakin share fage na gasar Kofin Zakaru na Hukumar wasan kwallon kafa ta Afirka na 2018.
Wani makaho dan asalin Pakistan yana wasannin hawa duwatsu da wasu tsaunuka domin nuna cewa nakasa ba kasawa ba ce.
Wasannin Olympics na karkara da ake yi duk shekara a jihar Punjab Da ke Arewacin India, ya janyo dubban jama’a daga sassa dabam dabam na kasar. Wadanda suka shirya wasannin sun yi ne da nufin raya al’adun ‘yan Punjab domin nunawa ‘yan baya hanya.
Matsalar beraye da ta addabi birnin Tehran ta tilastawa Iran kafa dakarun kashe beraye domin fatattakarsu. Beraye sama da miliyan 2 ne hukumomi suka ce ke cin karensu babu babbaka a birnin, adadin da ake ganin ya wuce haka. Yawaitar zubar da shara a ko'ina itace musabbabin wannan matsalar.
An kaddamar da wani babban Kumbon SpaceX na ‘yan sama jannati a jiya Talata a gwajinsa na farko dauke da wata jar motar tsere tare a yunkurin tafiyar sai baba ta gani zuwa kololuwar duniyar Mars.
A wani matakin bunkasa yawon shakatawa, hukumomin Masar sun gayyaci Sultan Kosen, wanda ya fi kowa tsayi a duniya, da Jyoti Amge, wadda ta fi kowa gajarta a duniya, domin ziyartar Dalar Giza, makwancin Fir'aunoni masu yawa
An kammala musabakar karatun Al-Kur'ani mai girma a karamar hukumar Illela Jihar Sokoto inda aka gudanar da bikin da har Gwamnan jihar, Aminu Tambuwal ya samu halarta.
Masu bincike a jami'ar Tokyo a Japan sun kera mutum-mutumi mai sarrafa kansa kamar bil adam ta yadda ya ke dauke da abubuwa masu kwaikwayon irin ayyukan da gabobi da kasusuwa suke yi a jiki wadanda ke ba shi damar yin atusaye kamar su press up da makamantansu.
Tattaunawa Da B-Merry Dan Arewan Legas
Wani dan Bosnia, Elvis Cero ya kera wata 'yar motar da ake iya nadewa kamar akwati domin maganin cinkoso a manyan birane. Motar mai suna 'Go City' tana amfani da wutar lantarki kuma an saka mata tayoyin keke mara nauyi sannan kuma batirin motar yana rike caji har na tsawon sa'o'i biyar.
Yi Lodin Kari..