Yau Za'a Fafata A Wasannin Copa Del Rey 2016/2017

A cigaba da wasannin Copa Del Rey na shekarar 2016/17, na kasar Spain, yau za'a kece raini tsakanin Kungiyoyin kwallon kafa guda goma.

Kungiyar kwallon kafa ta Villarreal, zata karbi bakuncin Toledo

Las, Palmas, zata fafata tsakaninta da Kungiyar kwallon kafa ta Huesca, ita kuwa Real Sociedad zata kece raini da kungiyar Real Valladolid.

Malaga zata marabci Cordoba, daga karshe Atletico Madrid, zasu fafata da kungiyar kwallon kafa ta Guijuelo.

Za'a buga wasanninne a lokuta daban daban agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi.

Har ila yau jiya an buga wasa daya tilo da ya rage a bangaren Laliga 2016/2017 mako na Goma Sha shida

Athletic Club ta doke Celta vigo da kwallaye 2-1.

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Za'a Fafata A Wasannin Copa Del Rey 2016/2017