Shugaba Buhari Ya Bada Umurni A Biya Super Falcons Hakkinsu

Sakamakon rashin biyan 'yan kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta mata na Najeriya super falcons, ya jawo 'yan wasan sunyi zanga zanga har zuwa fadar shugaban Najeriya dake Aso villa a birnin tarayar Abuja.

Super Falcons sunyi zanga zangar ce sabanin alkawari da hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta yi na kin biyansu alawus dinsu na wasan da suka buga na cin kofin 'yan matan Afirka (AWCON) 2016, a can kasar kamaru inda suka samu nasarar lashe kofin da ci daya da babu tsakaninsu da 'yan matan kasar kamaru.

Amman daga bisani an shawo kan matsalar domin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin a biyasu hakkinsu, a cewar shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasa Alhaji Abba Kyari, inda yace shugaba Buhari ya umurci ma'aikatar wasanni da kuma ma'aikatar kudi ta tarayyar Najeriya da su gaggauta biyan kudaden.

A Kwanakin baya ne dai akaji ministan matasa da wasanni Solomon Dalung na cewar rashin tabbas na cin kofin shiya haifar da matsalar rashin tanadar kudin da za'a biya 'yan wasan.