Miliyoyin Amurkawa Ne Suka Fita Kallon Husufin Rana

Miliyoyin Amurkawa ne suka fito jiya domin kashe kwarkwatar ido game da husufin da rana tayi, abinda rabon da ganin irin haka tun shekaru 99 da suka gabata.

Wannan husufin dai ya faro ne tun jiya littini daga jihar Oregon, wanda hakan yasa zafin rana ya ragu ainun domin ko wata ya kare ranar.

An kiyasta cewa a kalla mutane kusan miliyan biyu ne suka yi tuki cikin wannan yanayi a jiya littini wanda ya faro tun daga jihar Oregon ya kai har tsakiyar Amurka, wato zuwa kudancin jihar South Carolina.