Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Cewar Masana, Nan Bada Jimawa Ba Za'a Samar Da Maganin Mantuwa


Sakamakon kididdigar wata kungiya mai fafutukar kariya ga cutar mantuwa, mai suna ‘Alzheimer’ a turance, sun gano cewa, kimanin mutane sama da milliyan arbain da hudu na dauke da wannan cutar a fadin duniya. Cutar dai na taba jijiyoyin kwakwalwa ne, inda take rage musu karfi, har ta kai ga mutun baya iya tuna komai.

Wasu masu bincike a jami’ar Glasgow dake kasar Scotland, a Jami’ar Lester ta kasar Ingila sun samo maganin dake dakilar da matsalolin kwakwalwa, da suka shafi mantuwa. Maganin mai suna ‘Allosteric ligands’ na aiki ne domin farfado da sinadaran gina jiki ‘Protein’ dake kwakwalwa mai suna ‘Hippocampus’ a turance, wanda tasirin shi a jikin dan adan ke raguwa yayin da cutar Alzheimer ke ci gaba da ta’azzara.

Wani masanin kwayar halittar jikin dan adam dake jami’ar Glasgow, Farfesa Andrew Tobin, shine ya jagoranci aikin wannan kididdigar wacce aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ‘Clinical Investigation’ Farfesa Tobin, ya kara da cewar maganin na iya tsawaita rayuwar bera. Magungunan da ake amfani dasu yanzu anyi su ne domin rage alamomin cutar, amma masu binciken sunce aikin su yana maida hankali ne akan magance cutar baki daya.

Masu binciken sun yi gwajin maganin ne akan bera, inda suka saka mishi cutar ‘wild cow’ wacce take tamkar cutar mantuwa a jikin dan adam. Sakamakon nasu ya nuna alamun nasara domin berayen da aka bawa magani, sun iya tuna abubuwan da suka wuce, kana wadanda kuma ba a bawa magani ba, basu iya tuna komai ba. Tobin, ya kara da cewa wannan ba magani ne na yanzu-yanzu ba, domin zai dauki kimanin shekaru biyar zuwa goma, kafin a fara amfani da shi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG