Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakamata Mata Su Yunkuro Aikin Noma


An bukaci mata su rugumi aikin gona da kayan zamani domin rage wahalhalun noma da samarda amfanin gona mai yawa, Aisha Ibrahim Abubakar, wata mai ilimin Noma, ce ta furta haka a wata ganawa da suka yi da wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir.

Ta ce tana da burin ganin cewa mata su shahara a harkar noma, hasali shi yasa ta karanci aikin noma a jami’a Usman Dan Fodio dake Sokoto domin ta taimaka ganin hakan ya kasance.

Ta kara da cewa ta karanci harkar noma ne da zummar jan hankalin mata ga harkar noma, duk da cewar mafi akasari maza ne suka mamaye karatun aikin gona. Ta ce ya zama dole ta yi shi domin nunawa mata babu karatun da mace ba zata iya yi ba.

Aisha ta ce ta fara karantar Noma a Kaduna ne inda ta yi diploma daga bisani ta samu nasara ta tafi garin Sokoto domin cika burinta na samun digiri a aikin Noma.

Aisha ta ce kamar kowanne namiji da yayi wannan karatun suma sai da aka basu gona suka noma tun daga gyaran gonar har zuwa gribe albarkar noma, ta kara da cewa kalubalen da ta fuskanta bai wuce nisan cikin gari zuwa makaranta ba domin tana da auren ta koma makaranta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG