Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matashi Dan Najeriya Ya Kashe Budurwarsa A Kasar Jamus


An gurfanar da wani dan Najeriya, Anthony, mai shekaru ashirin da takwas (28), a gaban kuliya a kasar Jamus, inda ake tuhumarsa da laifin kashe budurwarsa Soopika Paramanathan, mai shekaru ashirin da biyu (22).

Anthony wanda ya kasance mai neman mafaka a kasar ta Jamus, ya yi ikirarin cewa shi dan luwadi ne kuma ya yi gwagwarmayar yakar kungiyar Boko Haram, ya kashe buduwar tasa ne baya ta ce ta sauwa ke masa samartakan.

Mai gabatar da karar ya ce Anthony, yawiwa budurwar tasa kisan wulakanci sanadiyar tsagwaron kishi inda ya soketa da wuka fiye da sau hamsin (50), a kanta da wuya da kuma nononta.

Shugaban ‘yan Sanda Harbert Mengelkamp, wanda ya maida hankali akan batun neman mafakar da Anthony ke fafutuka yace hukumomin na kokarin hana shi mafakar da yake nema’Shi dai Anthony an kamashi ne kwanaki biyu bayan da ya aikata kisan tashar Basel bayan da ya gudu zuwa kasar Switzerland.

Idan aka sameshi da laifin zai fuskanci daurin rai da rai a ranar da ake sa ran sauraren karar 20, ga watan Satumbar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG