Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Paris Saint German, tana daf da sayen matashin dan wasan nan dan kasar Faransa Kylian Mbappe mai shekara 18, da haihuwa, akan zunzurutun kudi har Fam miliyan £180. daga kungiyar Monaco.

Arsenal tace har yanzu hankalinta bai kwantaba, ganin dan wasanta Alexis Sanches, bai kara sabunta kwangilarsa a kungiyar ba, ganin saura shekara guda dan wasan ya kammala kwangilarsa a Arsenal.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho, yace yana da bukatar Karin ‘yan wasa biyu musamman dan wasan baya na gefen hagu Danny Rose, na Tottenham, da kuma dan wasan tsakiya na gefe Ivan Pericis, daga kungiyar Inter Milan.

Shi kuwa dan wasan tsakiya na Chelsea dan kasar Brazil William ya nuna sha'awarsa na komawa Manchester United inda yace yafi jin dadin wasa a karkashin Mourinho.

Tana iya yuwar Zlatan Ibrahimovic, ya sake rattaba hannu a kungiyar Manchester United bayan da sauran wa’adinsa na shekara daya ya kare a kungiyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Borussia Dortmund ta bukaci Barcelona da ta biya fam miliyan £135 in har tana son dan wasan gabanta Ousmane Dembele, wanda zai maye gurbin Neymar a Barcelona.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG