Ingila Na Kan Hanyar Kafa Tarihi

Liverpool da Manchester United

Hasashe na nuni da cewar Kungiyoyin kwallon kafa biyar daga kasar Ingila za su iya samun nasaran zuwa wasan zagaye na gaba watau (Round of Sixteen) a turance na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai na bana a karo na farko a tarihin gasar.

Amma sai idan Manchester United da Liverpool sun samu nasara wasannin da zasuyi na karshe a rukuni a wannan makon.

Manchester United ita take jagorantar rukunin (A) da maki 12, a yau talata zata buga wasanta na karshe da CSKA Moscow a kasar Ingila,

Liverpool itama tana mataki na daya ne a rukunin (E) da maki 9, inda gobe zata buga wasanta da Spartak Moscow.

Idan har kungiyoyin biyu suka samu nasara a wasanin da zasuyi sun shiga sahun kungiyoyin Chelsea, Manchester City da Tottenham wadda tuni suka samu tikitin haye zuwa wasan mataki na gaba.

Your browser doesn’t support HTML5

Ingila Na Kan Hanyar Kafa Tarihi - 2'35"