Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar kula da Kwallon Kafa Ta Ingila Ka Iya Tsawaita Hukunci Kan Paul Pogba


Hukumar dake kula da kwallon kafa ta kasar Ingila (FA) ta ce da yuwar za ta kara tsawaita hukunci kan dan wasan tsakiya na Manchester United mai suna Paul Pogba, wanda aka bashi Jan kati (Red Card) kai tsaya a wasan da Manchester, ta yi tsakaninta da kungiyar Arsenal.

Manchester ta bi Arsenal har gida ta doke ta da ci 3-1 a gasar Firimiya lig mako na goma sha hudu ranar Asabar inda sakamakon Jan katin da aka ba dan wasan bazai samu damar fafatawa a wasanni uku da Manchester, zata yi ba a kasar Ingila.

Hukumar ta ce tana sauraron rahoto daga wajan Allakalin da ya hura wasan inda ake tunanin ya sake aikata laifi bayan an bashi Jan katin, idan haka ta tabbata hukumar ta ce zata kara masa yawan wasanin da bazai buga ba akan wasanni uku.

Paul Pogba, bazai buga wasannin da Manchester, zata yi da Bournemouth da kuma Westbromwich ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:03 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG