Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Farautar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A bangaren hada hadar cinikayyan ‘yan wasan kwallon kafa ta duniya wadda za'a bude a watan Janairu 2018, kungiyar Newcastle tace tana kan bakanta na ganin ta sayo dan wasan baya na Manchester United Luke shaw amma bazata biya fam miliyan £20, ba.

Ita kuwa Arsenal tana zawarcin mai tsaron baya na Westbromwich ne mai suna Jonny Evans mai shekaru 29, a watan na Janairu.

Itama Manchester City tana zawarcin dan wasan tsakiya na Liverpool Emre Can mai shekaru 23, wanda shi kuma yace ya shirya tsaf don sake rattaba hannu a kungiyar.

Kungiyar Real Madrid tace zata maida hankalinta kan mai tsaron raga na Athletic Bilbao, Kepa Arrizabalaga mai shekaru 23, maimakon David De Gea na Manchester United.

Barcelona zata maida hankalin wajan ganin ta dauko dan wasan tsakiya na Chelsea William mai shekaru 29, in har bata samu dauko Philippe Coutinho ba.

Tottenham tana zawarcin dan wasan tsakiya na Westham mai suna Manuel Lanzina mai shekaru 24, da haihuwa, ita kuwa Barcelona tace tana bukatar Ozil daga Arsenal da yarjejeniya musaya a cinikin wacce tace zata bada Arda Turan a cikin harkar.

Manchester City tana shirye shiryen sabonta kwangilar dan wasan gabanta Raheem Sterling. Real Madrid tana neman dan wasan gaba na RB Leipzig mai suna Timo Werner.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG