Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Everton Tayi Sabon Mai Horar Da 'Yan Wasan


Sam Allardyce
Sam Allardyce

Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta sanar da sunan Sam Allardyce, a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasanta aikin da zai yi da kungiyar na tsawon shekara daya da rabi.

Allardyce zai karbi fam miliyan £6 a duk shekara inda albashinsa a mako zai kasance fam dubu £115, inda zai karbi jimillar fam miliyan £9 a tsawon zamansa na watannin goma sha takwas a kungiyar.

Kungiyar Everton ta ce ta dauko Allardyce ne domin ya dawo da martaban kungiyar a idon duniya da kuma magoya bayanta,

Kungiyar ta Everton dai ta take wasannin goma sha hudu a gasar firimiya lig na kasar Ingila, tayi nasara a wasani hudu kunnen doki sau uku an kuma doketa a wasanni bakwai.Yanzu haka tana matsayi na goma sha uku ne a teburin Firimiya lig na kasar Ingila.

A ranar laraba 29/11/2017 kungiyar ta Everton ta lallasa Westham daci hudu da babu a gasar Firimiya lig inda dan wasan gabanta Wayne Rooney ya zurara kwallaye uku.

Kungiyar Westbromwich ta bayyana sanarwar daukan Alan Pardew, a matsayin sabon manajanta wadda ya maye gurbin Tony Pulis da kungiyar ta sallama,

Alan Pardew, zai ye aiki a matsayin mai horar da ‘yan wasan westbromwich na tsawon shekaru biyu da rabi.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG