Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salman Khan Da Priyanka Chopra Likafa Tayi Gaba


 Salman Khan da Priyanka Chopra
Salman Khan da Priyanka Chopra

Salman Khan da Priyanka Chopra sun sami shiga cikin ayarin mutane dari biyar a fadin duniya da suke taka rawa wurin tafiyar da masana’antar nishadantarwa ta duniya wacce ta kai adadin dalar Amurka triliyon biyu.

Wasu mutane goma daga Bollywood suma sun sami shiga wadanda suka hada da masu shirya fina finai Karan Johar, Aditya Chopra da kuma furodusoci Ekta Kapoor, Sidharth Roy Kapoor, Mukesh da Anil Ambani.

Sauran sune shugaban kamfanin Essel, Dr. Subhash Chandra da shuwagabanin kamfanin Zee, Punit Goenka, Kishore Lilla da Uday Shankur.

A wani sakon da hukumar zartarwa na Variety masu sa ido akan harkokin nishadin ta ruwaito cewa Salman Khan, Aamir Khan da Shah Rukh Khan, suke jan ragamar Bollywood masamman wajen samu kudaden shiga.

Sakon ya cigaba da bayani akan fim din Salman Khan, dake tafe da kuma ayyukan da kungiyarsa mai zaman kanta take gudanarwa na jin kai.

Ita kuwa Priyanka an yi batun nasarorin da ta samu a Bollywood da Hollywood masamman shirinta na talebijin mai suna Quantico, da kuma shirinta na kyautata rayuwar yara abinda yasa aka yi mata jakadiyar UNICEF ta yara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG