Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Zai Fadada Manhajar Gano Sauyin Halaiyyar Mutane Zuwa Wasu Kasashe


Facebook, zai fadada manhajarsa dake gano sauyin halaiyar mutane zuwa wasu kasashe, bayan samun nasarar gwajin gano mutanen dake da niyyar kashe kansu da aka yi a Amurka.

Tun cikin watan Maris Facebook, ya fara gwajin wannan manhaja, lokacin da ya fara duba abubuwan da mutane ke kafewa a shafinsu, da kuma sharhi da mutane ke rubutawa don zakulo wata alama dake nuna cewa kalaman wani ko wata alama ce ta masu son kashe kansu.

Duk da yake Facebook, bai bayar da wani cikakken bayani a kan wannan shiri ba, amma ya ce manhajar tana bincikar wasu kalmomi dake zama alamu, kamar tambayoyi irinsu: “Lafiyar ka kuwa?” da “Zan Iya Taimaka Maka?”

Idan manhajar ta zakulo wani abu da ta yi imanin alamun tunanin kashe kai ne, zata sanar da ma’aikatan Facebook, wadanda suka kware wajen tunkarar ire-iren wannan rahoto.

Wasu lokuta tsarin kan baiwa mutune shawarar abin da yakamata su yi, ko ya sanar da abokansu abin da ke faruwa. Wasu lokutan ma ma’aikatan Facebook, kan ankarar da jami’an tsaro don daukar mataki.

A cewar mataimakin shugaban gudanar a aiyuka na Facebook, Guy Rosen, kamfanin ya yanke shawarar fitar da manhajar ne zuwa sauran kasashen duniya bayan da aka gudanar da gwaji aka kuma sami nasara.

Haka kuma Facebook, zai yi kokarin ‘daukar kwararrun ma’aikata da zasu rika kula kuma suna sanar da jami’an tsaro ta hanyar amfani da yare irin na yankin da suke.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG