Guguwar Musayar Zaratan 'Yan Wasan Kwanlo Na Ci Gaba Da Turnikewa

Dan wasan Gaba na Manchester united Anthony Martial, ya ki amincewa ya sabunta kwantirakinsa a kungiyar inda haka ke nuni da cewar dan wasan mai shekaru 22 haihuwa na iya barin kungiyar a karshen kakar wasan bana.

Tuni dai kungiyar Real Madrid, ta nuna sha'awarta ta dauko dan wasan zuwa kulob dinta. Kungiyar Chelsea, Manchester united da Everton suna duba yuwuwar dauko dan wasan gaba na kasar Brazil, mai taka leda a kungiyar Watford, mai suna Richarlison, dan shekaru 20 a duniya.

Har ila yau Everton da Westham sun shiga sahun zawarcin tsohon dan wasan tsakiya na Manchester united, Shinji Kagawa, wanda yanzu yake kungiyar Borussia Dortmund.

Wakilin dan wasan tsakiya na Manchester united Paul Pgoba, ya ce tun a watan janairu da ta gabata kofa take bude a kungiyar Real Madrid da Manchester City kan sayen dan wasan.

Atletico Madrid, zata kara albashin dan wasan gabanta Antoine Griezmann, zuwa fan dubu 300 duk sati domin ya cigaba da zama a kungiyar ganin cewar Barcelona, ta matsa kaimi wajan ganin ta dauke dan wasan a karshen kakar wasan bana.

Shugaban kungiyar Roma James, Pallotta ya karyata rade radin da ake yi na cewar mai tsaron ragar kungiyar Alisson, mai shekaru 25 zai bar kulob din a karshen kakar wasan bana don komawa kungiyar Liverpool.

Shugaban kungiyar Juventus Marotta, ya ce yanason dan wasan tsakiya na kasar jamus wanda yake taka leda a Liverpool Emre Can, 24, da ya yanke shawara kan zuwan sa kulob din nan da kwanaki goma, dan wasan dai a yanzu haka ya tafi jinya har zuwa karshen kakar wasan bana.

Your browser doesn’t support HTML5

Guguwar Musayar Zaratan 'Yan Wasan Kwanlo Na Ci Gaba Da Turnikewa