Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pep Guardiola Ya Bukaci Kungiyar Sa Ta Yi Tsabtataccen Wasa


Kocin kungiyar Manchester city, Pep Guardiola ya ce ya zamo dole kungiyar ta yi tsabtataccen wasa don samun nasara akan kungiyar Liverpool da ta doke ta 3-0 a satin da ya wuce na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai (UCL) a matakin wasan dab da na Kusa da na karshe karawa ta farko da suka yi a gidan Liverpool a makon da ya wuce.

A yau talata ne za'a sake karawa ta biyu a gidan Manchester city, Guardiola ya ce yana da karfin guiwar zai samu nasara a wasan domin a cewar sa “muna da minti 90 da karin lokaci kuma abin da muka nuna a wannan shekara “muna ikirarin samun dama a cikin 'yan mintoci kaɗan”.

A bangaren sa Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce 'yan wasan sa sun nuna cewa 'yan adam ne domin sun yi kokari a wasan farko amma sun amince da cewa za su iya samun nasara a wasan da za su yi yau talata.

Ya kuma bayyana cewar ya san Guardiola Babban kwac ne a duniyar kwallon Kafa, amman akwai sa'a a wasa.

Da aka tambaye shi kan Dan wasan Mohammed Salah, wanda ya fice a wasan su na farko saboda rauni, Kocin ya ce ba zai ce komai ba amma dai sun yi atisaye tare da dan wasan a jiya litinin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG