Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Karrama Marigayi Rasheedi Yekini


Rasheedi Yekini
Rasheedi Yekini

A karon farko, Hukumar kwallon kafar gasar Premier League ta Najeriya na shirin ba da kyautar karramawa tsohon dan wasan Najeriya Marigayi Rasheedi Yekini, ga dan wasan da ya fi zira kwallaye a gasar premier league ta Najeriya.

Kyautar an kirkiro ta ne domin a karrama Yekini a matayin dan wasan Najeriya da ya fi ‘yan wasan Najeriya yawan kwallaye ga kungiyar Super Eagles a lokacin yana raye.

Yanzu haka ‘yan wasan da ke kan gaba da ake hassashen za su iya lashe kyautar sun hada da Tunje Adeniji an kungiyar Sunshine Stars, wanda ke da kwallaye 12 a raga.

Sai Bright Ejike na kungiyar Heartland mai kwallaye 11, sannna akwai Gbolahan Salami na Warri Wolves mai kwallaye tara.

Kana akwai Chisom Chikatara na Warri Warrios wanda shima ke da kwallaye tara. Sai Eksosa Igbanoba mai kwallaye takwas wanda ke taka leda a Nasarawa United da kuma Ndifreke Offiong mai kwallaye takwas shima wanda kuma ke bugawa Abia Warriors. Har ila yau akwai Shuiabu mai kwallaye 8 da ke bugawa Giwa FC.

XS
SM
MD
LG