Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PSG Zata Iya Zama Zakaran Champion Lig - inji Ibrahimovic


Zlatan Ibrahimovic
Zlatan Ibrahimovic

Zlatan Ibrahimovic ‘dan wasan kungiyar Paris Saint-Germain yace, baya tunanin barin kungiyarsa a karshen kakar wasan bana, kamar yadda ake tsammanin zai yi.

Ana dai alakanta ‘dan wasan mai shekaru 33 da haihuwa da cewa zai iya barin kulub dinsa zuwa AC Milan ko zai shiga jerin wasan lig lig na America wadda aka fi sani da MLS, amma ya fito ya nuna cewa shi yana farin ciki da ya ci gaba da wasa a kungiyarsa, duk da yake kwantaragin sa da kungiyar zai kare a shekara mai zuwa.

Lokacin da yake magana da manema labarai Ibrahimovic yace, “ina cikin farin ciki, ina kuma jin dadin a inda nake, ina kuma da sauran shekara daya da ta rage min nayi wasa da PSG.”

Idan aka duba dai a kakar wasan da ta wuce kungiyar ta PSG tayi nasarar ‘daukar kofuna, duk da dai bata sami zama zakaran Champion Lig ba. amma Ibrahimovic na da kwarin gwiwar zasu iya samun zama zakaran idan lokaci yazo, in har suka gyara wasu ‘yan kura-kurai a kungiyar su.

Dan wasan dai ya nuna cewa kaiwa ga zama zakaran Champion Lig na bukatar kula da wasu muhimman bayanai, wanda irin su sune ke tasiri idan aka hada da sa’a, kuma lokacin muna da kuzari yanda ake so, to zamu iya kaiwa ga zama zakara. Ya ci gaba da cewa, da alamu tawagar mu ta kai har zuwa karshe, amma ba abu ne mai sauki ba. zamuje wasan kuma zamu tabbatar mun baiwa sauran kungiyoyi wahala, wannan ya zama tabbas.

XS
SM
MD
LG