Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Kare Kambin ta a Kasar Chile {FIFA}


'Yan Kwallon U 17
'Yan Kwallon U 17

Kasashen Amurka da Mexico sun tsinci kansu a rukunin mutuwa a gasar cin kofin kwallo kafa na duniya na ‘yan kasa da shekaru 17, da za’a buga a kasar Chile.

Amurka, zata hadu da mai masaukin baki kasar Chile, da kasar Croatia da kuma Najeriya, a rukunin “A.”

Najeriya, dai ita ke rike da kofin a yanzu haka kuma tafi kowane kasar samun nasara a tarihin gasar na rukunin ‘yan kasa da shekaru 17.

Kasar Mexico wace ta zo ta biyu a bayan Najeriya, a gasar a shekarar 2013, zata hadu da kasashen Australia, Jamus da Argentina, a rukunin “C.”

Kasashen Hundurus, Belgium Mali and Ecuador zasu kasance a rukunin “D”

Inda Ticos da Afirka ta kudu, da Kuriya ta Arewa da Kasar Rasha zasu hade a rukunin “E”

XS
SM
MD
LG