Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayanai Kan Giroud Sun Saba wa Abinda Ya Faru, Inji- Arsenal


Kulob din Arsenal ya fito karara ya bayyana cewar jita-jitan da a ke ta cewar dan wasan ta Oliver Girad ya suma ranar lahadi a locacin da suka rasa wasan su da kulob din West Ham a lokacin bude wasan Premier League ba gaskiya bane.

Cheikhou Kouyate da Mauro Zarate ne suka jefa wa kulob din Hammers kwallaye inda suka ba ‘yan wasan na Gunners mamaki a filin wasan Emirate,

Amma kamar yadda mai marabtar wasan suka ci gaba da fama a lokacin wasan, dan wasan su Giroud ya tafka wani gagarumin karo tsakanin sa da James Tomkins a cikin minti goma sha shidda na wasan.

Dan wasan gidan na Arsenal ya fadi warwas ne kafin sauran abokan sa suka juya shi ta gefe a yayin da yake kwance.

Daga karshe duka ‘yan wasan biyu sun ci gaba da taka leda har zuwa karshen wasan bayan jiyyar da suka yi ta wani dan lokaci, ba tare da wani likita na musamman ya duba su ba kamar yadda Premier League ta bukata.

An soki kulob din na Arsenal da aje dan wasan na su Giroud a gefen fili amma yanzu sun fito sun kare kan su.

Hukumomin kulob din na Gunners ne suka aika da sako ta kafar zumuntar Twiter, cewar bayanai akan Giroud sun sabawa abin da ya faru a lokacin da ya yi karo a filin wasa, ba suma ya yi ba, dan haka ma, dan wasan ya koma gida lafiya kalau kamar yadda ya saba.

XS
SM
MD
LG