Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Baiwa Kananan Hukumoni Kudaden Domin Gudanar da Aiyuka


J
J

Mutanen da dama a kanana hukumomin Misau da Darazau , a jihar Bauchi sun rasa gidajensu sanadiyar ruwan sama haka kuma sun yi hasarar na kayayyakin gona kama daga shinkafa zuwa Masara.

Bayani daga kanana hukumomin biyu na nuni da cewa ruran sama ya malale Tituna daga bisani ya shiga gidajen jama’a, wanda hakan yayi sanadiyar rushewar gidaje a birane da kauyuka.

Mai rikon karamar hukumar Misau, Ado Sarkin Aska, yace ‘yan Majalisu na jihar da na tarayyaduk sun kawo taimako ga jama’ar da bal’in ya shafa.

Shima mai rikon karamar hukumar Darazau, Malam Mustapha Zalami, yace suna bukata daukin kayan aiki kamar kwanon rufi da katako da kuma Siminti da kuma kayan abinci.

Dan Majalisar mai wakilitar karamar hukumar Kirfi Ibrahim Galadima, ya bukaci ganin an baiwa kananan hukumoni kudaden su domin gudanar da aiyuka ga mutanen su kamar yada yakamata a kasancewar su matakin Gwamnati na ukku.

XS
SM
MD
LG