Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaji Sun Sha Wuta a Jihar Neja


Kaji
Kaji

Hukumar Kwastam a Najeriya ta kona naman Kaji da ake shigowa da shi daga kasashen waje a jihar Neja, dama dai tuni Gwamnatin Najeriya ta hana shigowa da irin wannan nama cikin kasar.

Shugaban Kwastam mai kula da shiryar ta biyu mai ofis a Kaduna, Mr.Ajiya Masiah, ne ya jagoranci kona Kajin.

Ya kuma ce “Gwamnati ta hana kawowa wadannan abubuwan dan haka dole ne mu tsayarda shi saboda illar da yake yi ga bil- Adam, an samu wadanna ne ta bayanai na siri da hukumar ta samu ne tsakanin Jebba da Mokwa.”

Wanda aka kama Kajin a motarsa Sirajo Adamu, ya yiwa wakilin muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari, bayani cewa shi bai san cewa an yiwa motarsa lodi da Kaji ba.

A wani makeken rami ne aka suba naman Kajin sanan aka banka wuta a gaban sauran jami’an tsaro da suka hada da ‘yan Sanda da kuma jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA.

XS
SM
MD
LG