Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tijjani Babangida Ya Zama Mataimakin Sunday Oliseh


An bayyana sunan tsohon ‘dan wasan Super Eagles Tijjani Babangida, a matsayin mataimakin Sunday Oliseh na musamman kuma mai bada shawara.

Baki ‘dayansu Babangida da Oliseh a baya sunyi wasa tare a kungiyar Ajax Amsterdam dake Holland, tun wannan shekarun sun dai rike dangantakar su mai kyau.

Za dai a bude filin horon ‘yan wasan Eagles cikin mako mai zuwa a Abuja, ana kuma tsammanin cewa Babangida zai hadu da tawagar ‘yan wasan, alokacin da zasu fara shirye-shiryen wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za’a yi watan Satumba mai zuwa a kasar Tanzania.

Babangida dai yana da kwarewa wajen iya horas ‘yan wasa, kamar yadda ya jagoranci kungiyar FC Taraba, a wasan Firimiya lig wadda ta sami nasara a fafatawar da tayi shekaru biyu kenan da suka wuce, ta dai zama zakara wanda bata taba ba a baya.

XS
SM
MD
LG