Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Kaddamar Da Fim Dauke Da Tarihin Rayuwar Tiger Woods


Fittaccen dan wasan kwaikwaiyo na kasar Amurka Alex Gibney, ya bayyana kudirin shi na fitar da wani sabon fim wanda ke dauke da tarihin rayuwar shahararren dan wasan kwallon rami Golf, Mr. Tiger Woods.

Tiger, shine mutun daya tillo da ya taba lashe kambun zarata a fagen wasan golf a jere sau goma sha hudu 14. Za’a tace labarin daga littafin tarihin dan wasan da aka kaddamar jiya Talata.

Ya zuwa yanzu dai basu sanar da zuwa yaushe ake sa ran fitowar fim din ba, shidai Tiger mai shekaru 42, wanda yayi fice a wannan karnin na 21, rayuwar shi ta kasance mai cike da abubuwan ban sha’awa.

Tun bayan dawowar shi daga hutun jinya da yayi na wani aiki da aka yi masa, a gadon bayan, yana kokarin ganin ya sake maye gurbin sa na zakaran gwajin dafi a fagen wasan wasannin golf.

Dan wasan dai bai zanta da manema labarai ba, amma ya umurci mai magana da yawun sa ya basu duk wani ba’asi da suka bukata, littafin nasa da aka sayar ya samu karbuwa a shafin kasuwar Amazon, kuma mutane sun yaba da yadda labarin ya kasance.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG