Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ryan Bertrand Ya Fice Daga Ya Fice Daga Tawagar 'Yan Wasan Ingila


Dan kwallon Arsenal, Jack Wilshere, ba zai buga wasan da Ingila zata yi da kasar Netherlands ba awasan sada zumunci a yau Jumma'a bayan ya samu rauni a guiwarsa lokacin da yake karban horo.

Amma kocin kungiyar Southgate, ya ce yana fatan "Wilshere" zai samu damar fafatawa a wasan da kasar sa za ta buga da takwararta ta kasar Italiya a Wembley.

Wilshere ya shiga cikin tawagar Ingila a karo na farko tun a shekarar 2016.

Sai dai Mai horas da tawagar ‘yan wasan Ingila, southgate ya bayyana cewar raunin ba mai tsanani bane, dan haka yana da tabbacin dan wasan zai iya samun sauki kafin wasansu na gaba da Itali.

Dan wasan baya na Tottenham, Ryan Bertrand ya fice daga tawagar ‘yan wasan Ingila wanda zasu fafata a wasan sada zumunci da kasar Itali da Netherlands sakamakon ciwon baya da yake damunsa.

Dan wasan zai dawo kungiyarsa ta Tottenham don ci gaba da kulawa game da lamarin, Kasar ta Ingila zata buga wasan sada zumunci tsakaninta da kasar Netherlands ranar Jumma'a, 23 Maris da kuma Itali a Wembley a ranar Talata 27 ga watan Maris.

Shi kuwa Dan wasan Manchester United, Alexis Sanchez, ya kasance a sansanin tawagar ‘yan wasan kwallon kafa na Chile a shirin da ta ke yi na buga wasan sada zumunta da kasar Sweden.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG