Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al Khartoun Ta Kori Emmanuel Amunike A Matsayin Kocin Ta


An kori tsohon dan wasan Najeriya Emmanuel Amunike, a matsayin kocin kungiyar Al Khartoum SC ta kasar Sudan sakamakon rashin tabuka wani abin kirki a yayinda yake jagorancin kungiyar.

Amunike, Tsohon manajan tawagar ‘yan wasan Najeriya, ne ‘yan kasa da shekaru ashirin (U20) ya koma Al Khartoum, ta kasar Sudan a matsayin mai horaswa a watan Nuwamba 2017, a kan yarjejeniyar kwantirakin shekara daya.

Ya samu nasarar sakamako masu kyau a wasanni da kungiyar ta yi a karkashin sa kafin kakar wasannin lig din kasar Sudan, amma daga baya, ya fuskanci rashin samun sakamako mai kyau a wasannin lig inda da suka sami maki 11 daga wasanni takwas a gasar Premier ta kasar Sudan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG