Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Siyasar Yankunan Ku Na Cika Alkawuran Da Suka Yi Wa Matasa?


Masu iya magana sun ce an dade ana ruwa kasa na shanyewa, shugabannin siyasa sun dade suna shafawa matasa mai a baki ta hanyar yi masu alkawurra iri daban daban amma har yanzu shiru kamar an shuka dussa a wasu wuraren. Ya ya wannan lamarin yake a yankunan ku?

Muna bukatar sakonnin maza da mata akan wannan tambaya, kuma za’a iya aiko mana da sakon ta murya a kafar sada zumunta ta WhatsApp mai lamba +12025775834. Kada a manta a fadi suna da kuma jiha ko gari.

Ana iya sauraren wannan shiri a duk lokacin da ake bukata a shafinmu mai adireshi www.dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG