Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa Sun Kashe Mahifinsu A Jihar Kano


Wata kotun Majistare a Kano, ta bukaci da a tsare wasu ‘yan uwa Rabiu Adamu, mai shekaru ashirin da bakwai (27) da Auwal Adamu, mai shekaru ashirin da shida(26) a bisa zargin cewa sun kashe mahaifinsu Adamu Gamji, mai shekaru hamsin da biyar (55).

Su dai wadannan matasa sun aikatawa mahaifinsu wannan aika aika ne a karamar hukumar Sumaila a bisa zargin cewa shi mahaifin nasu Adamu Gamji, yana da hannu a mutuwar wasu ‘yan uwansu uku, da kuma rashin lafiyar da wani mai suna Sale Adamu ke fama dashi.

Ana tuhumar matasan ne da laifin hadin baki da na kisan kai a karkashin sashe na tasa’in da bakwai (97) dana dari biyu da ashirin da daya (221) na kundin laifuffukan jihar Kano.

Dan Sanda mai gabatar da kara, Pogu Lale, ya fadawa kotu cewa a ranar 24, ga watan Satumban da ta gabata ne wadanda ake tuhumar suka hada baki da wasu mutane ‘yan uwansu su shida wadanda hukuma ke nemansu ruwa a jallo domin kashe Adamu Gamji.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG