Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daukar Matakan Hana Ramuwar Gayya Wajibi


Shamaki Peter
Shamaki Peter

An bukaci gwamnatin jihar Plateau, da ta dauke tsauraran matakan dakile duk wani yunkurin na ramuwar gayya a rikice rikicen da ya faru a karamar hukumar Bassa dake jihar Plateau.

Shugaban gamayyar kungiyoyin masu zaman kansu Shamki Peters, ne ya yi kira a wani hira da dandalinvoa, yace ganin cewa duk da dokar hana fita daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe aka kai harin da ya halaka fiye da mutane ashirin da biyar.

Shamaki, ya buka ci matasa dasu kauracewa duk wani dan siyasar da ya bukaci yi amfani dasu domin tada fitina, yana mai cewa idan har suka yarda aka yi amfani dasu to su to tabaci hakika zasu koka nan gaba.

Ya kara da cewa duk idan babu zaman lafiya toh tabaci hakika babu wani cigaba mai ma’ana da zai zowa yankin saboda haka ya umarci matasa dasu tabbatar da cewa zaman lafiya ya wanzu a duk ida suke.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG