Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Fafata A Farkon Gasar Wassanin Firimiya Lig Na Najeriya


A ranar Asabar 13 ga watan Janairu na shekarar 2018, aka fara gasar Firimiya lig ta tarayyan Najeriya wato Nigerian Professional Football League, inda aka fafata tsakanin kungiyar Katsina United da takwararta Kano Pillars, a filin wasa dake Katsina. An dai tashi a wasan Katsina united Nada 2 Kano Pillars 2,

A ranar lahadi kuwa 14/1/2018 an ci gaba da sauran wasannin inda aka buga wasanni tara a jihohi daban daban, ga kuma sakamakon wasannin;

Kwara United 0-2 Niger Tornadoes

Abia Warriors 2-0 MFM FC

Wikki Tourists 1-0 Go-Round

Akwa United d 2-0 Rangers

Rivers utd 1-0 Elkanemi Warriors

Heartand 0-0 Sunshine stars

FC IfeanyiUbah 2-1 Yobe Stars

Lobi Stars 1-1 Enyimba

Nassarawa United 0-1 Plateau United

Ga kuma sunayen 'yan wasan da suka jefa kwallo a raga a makon farko a gasar.

Ndifreke Effiong daga ABIA Warriors kwallaye 2

Sauran wadannan sunaye na kasa duk kansu kowa ya jefa kwallo daya a wasan.
Junior Lokosa - Kano Pillars

Ibrahim Al-Hassan - Kano Pillars

Chinedu Ajanah - Katsina United

Destiny Ashadi - Katsina United

Eric Frimpong - Niger Tornadoes

Ibrahim Babawo - Niger Tornadoes

Chinedu Udeagha - Enyimba

Kelly Kester - AKWA United

Dennis Nya - AKWA United

Godwin Obaje - FC IFEANYIUBAH

Sola Dada - FC IFEANYIUBAH

Nafiu Kabuga -Wikki Tourist Fc

Ezekiel Mba - Lobi Stars

Guy Kuieman - Rivers United

Ohanacham - Yobe Desert Stars

Raphael Ayagwa - Plateau United.
Sannan kuma a wasanni goma da aka buga kulob biyar sun samu nasara a gida, Kungiyoyi uku kuma sunyi kunnen doki, Guda biyu kuma sun sami nasara a waje

Sai ranar 16/1/2018 za'a fafata a wasan mako na biyu mai taken wasan tsakiyar mako.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:29 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG