Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wilson Oruma Ya Samu Tabin Hankali


Wilson Oruma

Tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafar Najeriya, Super Eagles, Wilson Oruma, ya samu kushewar hankali, abinda ake danganta shi da damfarar da akace wani Fasto ya yimasa na makuddan kudade.

Oruma, wanda yayi zamani da ‘yan wasan Najeriya irinsu Jay Jay Okocha da Kanu Nwankwo, a yanzu ya fada manja, kuma yana fama da lallura tabin hankali, bayan da ake zargin cewa an damfareshi game da wata harka ta mai.
An ce ya yi hasarar kimanin Naira miliyan dubu da dari biyu, wani amininsa Emakpor Dibofun, ya fadawa mujallar Complete Sports, cewa har yanzu dan wasan bai farfado daga magagin hasarar da yayi ba sakamakon mumunar damfarar da akayi masa.

Ya kara da cewa dan wasan ya je wurare da dama domin neman mafita amma bata sake zani ba.

Dan wasan dai ya bugawa Najeriya, a matakin ‘yan kasa da shekaru 17, ‘yan kasa da shekaru 23 da kuma Super Eagles, ya kuma kasance cikin ayarin wadanda suka lashe gasar FIFA na ‘yan kasa da shekaru 17, wanda aka yi a 1993 da wadanda suka lashe gasar Olympic na 1996.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG