Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hrithik Roshan Ya Doke Shah Rukh Khan Da Sauran Jaruman Bollywood


 Hrithik Roshan
Hrithik Roshan

A shekarar 2017, an ga fina finai masu karatarwa a Bollywood daga jarumai daban daban inda bajintar wasu ya kayatar wasu kuwa hubbasansu ya jan hankulan masu kallo domin karbuwar da samun jinjina daga garesu.

Domin sanin jarumin da jama’a suka fi yin amanna da fina finansa an bukaci jama’a dasu kada kuri’a domin haka, kuma sakamakon bay kasance da mamaki ba duk da kasancewar fitattun jarumai ne suka yi gogayya da juna kuma jama’a sun zabe wanda suka fi gamsuwa da fina finansa.

Hrithik Roshan ne Jama’a suka zaba inda ya lashe kashi sittin da takwas cikin dari na yawan kuri’un da aka kada domin kasancewa fitatcen jarumin shekara 2017, na jaruman Bollywood, ya samun nasarar lashe zaben ne dalilin fim dinsa mai suna Kaabil, fim din da ya taka rawar gani a tsakiyar shekarar 2017, inda jarumin ya fito a matsayin makaho, wannan fim din ya samu karbuwa daga jama’a da masu nazarin fina finai kamar yaro yaso waje.

Hrithik Roshan, ya doke Shah Rukh Khan, Akshay Kumar, Salman Khan da Varun Dhawan domin lashe wannan kambi na jarumin da yafi kowane jarumi karbuwa a Bollywood. Hakika bajintar da ya nuna a fim dinsa na Kaabil jama’a, sun ayyana cewa zai lashe takarar domin irin hazakar da ya nuna a cikin fim din na Kaabil.

Shah Rukh Khan shi ya zo na biyu da kashi goma sha shida a cikn dari na yawan kuri’un da aka kada sai Salman Khan yazo na uku , inda Akshay kumar da Varun Dhawan suka yi kunnan doki a na hudu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG