Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Alexis Sanchez

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tana zawarcin dan wasan gaba na Leicester city Riyad Mahrez 26, sai dai dan wasan yafi sha'awar da ya koma kungiyar Arsenal maimakon Liverpool.

Manchester United ta Saka fam miliyan £25 akan dan wasan Arsenal Alexis Sanchez, sai dai Sanchez hankalin yafi karkata zuwa Manchester City inda ita kuma ta saka fam miliyan £20.

Ita kuwa kungiyarsa ta Arsenal tana neman a biyata fam miliyan £30 ga duk kungiyar da take bukatar dan wasan.

Carlo Ancelotti shi ne ake ganin zai maye gurbin Arsene Wenger a Arsenal in har Wenger ya kammala aikinsa a kungiyar.

Barcelona ta cimma yarjejeniya kammala ciniki tsakaninta da kungiyar Palmeiras' kan sayen dan wasan bayanta Yerry Mina akan kudi fam miliyan £10.8.

Dan wasan dai zai maye gurbin Javier Mascherano. ne a kungiyar inda yanzu haka dan wasan ke shirye shirye tafiya kasar Spain domin kammala komawarsa Barcelona.

Mataimakin shugaban kungiyar Fulham Tony Khan yace kungiyar bazata sayar da matashin dan wasan bayanta na gefen hagun ba mai suna Ryan Sessegnon dan kasar Ingila a watan Janairu nan duk dacewar Manchester United da Tottenham sun nuna sha'awarsu na ganin sun dauki dan wasan mai shekaru 17 da haihuwa zuwa Kulob dinsu.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG