Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Football Soccer - Germany v Italy - International Friendly - Allianz-Arena, Munich, Germany - 29/3/16 Germany's Mesut Ozil scores the fourth goal by a penalty REUTERS/Michael Dalder - RTSCQM8
Football Soccer - Germany v Italy - International Friendly - Allianz-Arena, Munich, Germany - 29/3/16 Germany's Mesut Ozil scores the fourth goal by a penalty REUTERS/Michael Dalder - RTSCQM8

Tsohon dan wasan Inter Milan da Real Madrid Sneijder mai shekaru 33, ya koma kungiyar kwallon Kafa ta Al-Gharafa. dake kasar Qatar, inda ya rattaba hannu a kwangilar shekara daya da rabi.

Kafin komawarsa dan wasan ya buga wasa a Kungiyar Nice ta kasar Faransa bayan ya bar kungiyar Galatasaray a watan yuli, dan wasan yanuna jin dadinsa da komawa kasar ta Qatar tare da iyalan sa

Jese Rodriguez, 24, na daf da hadewa da kungiyar kwallon Kafa ta Las Palmas

a kasar Spain, dan wasan a yanzu haka yana taka Leda a kungiyar kwallon Kafa ta Stoke City ne a matsayin aro daga PSG.

Liverpool tana kokarin ganin ta dauko dan wasan Monaco Thomas Lemar domin ya maye gurbin dan wasanta Philippe Coutinho wada ya koma Barcelona.

Leicester City na daf da sayen dan wasanta na farko a watan Janairu nan dan kasar Mali mai suna Fousseni Diabate, mai shekaru 22, akan kudi fam miliyan £1.7.

Dan wasan tsakiya na Shakhtar Donetsk dan kasar Brazil Fred, mai shekaru 24 yace yana jiran kira ne kawai daga kungiyar Manchester City, Newcastle United tace tana da karfin gwiwa wajan kammala sayen dan wasan gefe na Chelsea mai suna Kenedy dan shekaru 21.

Liverpool na zawarcin dan wasan tsakiya daga kungiyar RB Leipzig Naby Keita mai shekaru 22, tace zatayi duk yadda zata iya wajan ganin sayen dan wasan a watan Janairu nan.

Juventus tabi sahun Manchester United wajan zawarcin Mesut Ozil daga kungiyar Arsenal Juventus tace zatayi amfani da babban abokin Ozil Sami khedira domin ya jawo hankalin dan wasan kan ya dawo kulob din da taka Leda Chelsea tana zawarcin dan wasan gaba na Borussia Monchengladbac mai suna Thorgan Hazard, mai shekaru 24.

Dan wasan gefe na kasar Brazil mai taka Leda a kungiyar kwallon Kafa ta PSG Lucas Moura na bukatar barin kungiyarsa ta PSG domin komawa Manchester United.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG