Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coutinho Ya Matsa A Kan Liverpool Ta Sayar Da Shi Ga FC Barcelona


Philippe Coutinho
Philippe Coutinho

Philippe Coutinho ya sake nanata kwadayinsa na barin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool zuwa FC Barcelona, a cinikin dan wasan da watakila zai zamo mafi tsada a tarihin Firimiya LIg na Ingila.

Sau uku kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona ta yi kokarin sayen dan wasan mai shekaru 25 da haihuwa, amma Liverpool tana kin wannan tayin a kakar hada-hadar 'yan wasa ta lokacin zafi a 2017, amma duk ba a karbe su ba. Tayin karshe da ta yi, shine na tsabar kudi Fam miliyan 82, inda aka kuma makala wasu 'yan tanade-tanaden da idan dan wasan ya cika su kudin zai iya haurawa zuwa Fam miliyan 118.

Tun a wancan lokacin dai Coutinho ya mikawa Liverpool takardar cewa yana son a sayar da shi, kuma ganin irin rawar da a yanzu kulob din ke ba shi ya taka, yana jin cewa ya kamata lallai Liverpool ta amince ta kyale shi ya koma wata kulob dabam, musamman idan aka yi mata tayin da zai zarce na Fam miliyan 89 da Manchester United ta biya domin sayen Paul Pogba daga kungiyar Juventus.

Wasu majiyoyi na kusa da Coutinho sun ce Liverpool ta yi kokari, amma a banza, domin ta lallashi dan wasan dan kasar Brazil da ya canja ra'ayinsa ya zauna, har ma ta ce zata kara masa albashi.

Babban abinda yake kwadaita masa son komawa Barcelona shine shirin kulob din na sake gini a bisa harsashin irin kwarewarsa, kuma ganin cewa babu wani kofin da ya lashe tun zuwansa Liverpool, yayi imani da cewa lokaci yayi da zai koma inda yake da damar lashe kofuna. Aka ce 'yan'uwansa ma sun bayyana masa goyon bayansu ga yin hakan.

Liverpool zata fi jin dadin rabuwa da dan wasan nata idan har kungiyar Barcelona, mai fama da tarnaki na kudi, zata iya gabatar mata da tayi mai tsokar da ba zata iya ce a'a ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG