Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Na Gogayya Wajen Zawarcin 'Yan Wasa


 Philippe Coutinho
Philippe Coutinho

Chelsea tace tana da sha'awar dauko Rossy Barkley mai shekaru 24 daga Everton da kuma Thomas Lemar mai shekaru 22, na Monaco a watan Janairu.

Arsenal da Liverpool sun hade wajen zawarcin dan wasan tsakiya na Real Madrid Dani Ceballos, dan shekaru 21, Valencia kuwa ta amince ta biya fam miliyan £31, domin sayen dan wasan gefe na PSG mai suna Goncalo Guedes, mai shekaru 21.

Westham Crystal palace da Westbromwich suna zawarcin mai tsaron raga na Manchester United Sam Johnstone mai shekaru 24, wadda yake aro a kungiyar Aston Villa.

Everton da Arsenal na zawarcin Steven N'zonzi daga kungiyar Sevilla, tsohon dan wasan tsakiya na Stoke City mai shekaru 29, ya shaida wa kungiyarsa ta Sevilla cewar yana son canja sheka.

Barcelona tana shirin cere zunzurutun kudi har fam miliyan £132, domin dauko Philippe Coutinho daga Liverpool a watan da zaran an bude hada hadar ‘yan wasa.

Paulinho ya baiyana zuwa Coutinho Barcelona na da amfani sosai, inda wani kulob a kasar Sin mai suna Chongqing Dangdai ya ce baida niyyar dauko dan wasan tsakiya na Barcelona Andreas Iniesta, wanda ake ta rade raden dawowarsa kungiyar.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG