Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Bukatar Jose Mourinho Yayi Karin Bayani


Youths, who covered themselves in silver paint to become 'manusia silver' (silvermen) to make a living, laugh as they ride on the back of a truck in Jakarta, Indonesia.
Youths, who covered themselves in silver paint to become 'manusia silver' (silvermen) to make a living, laugh as they ride on the back of a truck in Jakarta, Indonesia.

Hukumar dake kula da wasannin kwallon kafa ta kasar Ingila (FA) ta bukaci mai horar da kungiyar Manchester United José Mourinho, da yayi mata bayanin kalamunsa da yayi ranar Jumma'a gabanin wasan da kungiyarsa tayi da Manchester City.

José Mourinho yayi wata magana da manema labarai ana saura kwana daya Manchester United ta kara da Manchester City a gasar Firimiya lig na bana, mako na goma sha shida 16.

Inda yace ‘yan wasan Manchester City suna amfani da wata dabara a lokacin da suke wasa sukan sake jikinsu kamar basu da karfi koda iska ya huresu sai kaga sun fadi don niman alkalin wasa ya taimakesu su samu nasara a wasan.

Dangane da wannan kalamai na Mourinho, ne hukumar FA take bukatar yazo ya mata cikekken bayanin abunda yake nufi da wannan magana tasa.

A wasan dai Manchester United ta sha kashi daci 2-1 a gidanta inda bayan an tashi a wasan akayi wata hayaniya tsakanin ‘yan wasa yayinda ‘yan wasan Manchester City suke rera wake na murnar a cikin dakin hutawan ‘yan wasa dake filin wasa na Old Trafford.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG