Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Yi Karon Batta A Bollywood


Dev Adhikari daya daga cikin jaruman Bollywood da ya fito a fim din nan mai suna Bengal, za a sako sabon fim dinsa mai suna Amazon Obhijaan, wanda ya kasance cigaban fim din Chander Pahar, wanda ya baiwa marada kunya a shekarar 2013.

Idan a wannan shekara fim din ya kasance wanda ya baiwa marada kunya toh ba a san abinda za a ce akan wannan sabon fim din ba.

Ranar ashirin da biyu (22) ga watan Disamba da za a sako fim din shine ranar da shima Salam Khan, zai sako nashi fim din mai suna Tiger Zinda Hai, inda zai yi kukan Damisa duk da zammar jan ra’ayin jama’a domin samun makudan kudaden.

Ana harsashen cewa Amazon Obhijaan, zai doke fim din Baahubali, kuma ba karamin fim ne zai iya doke tarihin da Baahubali ya kafa . Yanzu abinda ya rage shine musa ido mugani shin Amazon Obhijaan ko kuma Tiger Zinda Hai, wannene zai samu jan hakalin masu kalo.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG