Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zawarcin 'Yan Wasa Gadan Gadan


A bangaren hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na Duniya, kungiyar kwallon kafa ta Manchester City na daf da cimma yarjejeniya kan sabunta kwangilar dan wasanta Kevin De Bruyne, wanda ya zo kungiyar a shekara 2015 daga Wolfsburg à matsayin dan wasan da yafi kowa tsada a kulob din akan kudi £55.

Manchester Arsenal Chelsea na zawarcin dan wasan gefen baya na Crystal Palace Wilfred Zaha akan kudi fam miliyan £40.

Antoine Griezmann na shirin Koma kungiyar Barcelona da taka leda a shekara mai zuwa, ita kuwa Borussia Dortmund tace tana kan turbar ganin ta dawo da tsohon dan wasanta Henrickh Mkhitaryen daga kungiyar Manchester United.

Westham tana shirye shiryen dauko dan wasan gaba na Liverpool Danny Ings da kuma Harry Arter, dan wasan tsakiya na Bournemouth a watan Janairu nan.

Dan wasan gaba na Dortmund dan kasar Gabon Emerick Aubameyang ya kara tsawaita zaman sa a kungiyar ta Dortmund.

Shugaban kungiyar PSG yace ya zamo musu dole su shiga kasuwa a watan Janairu domin neman dan wasan tsakiya na baya Kasancewar dan wasan su Thiago Motta ya samu rauni a gwiwarsa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG